Skip to main content

Full text of "Muhimmin Jawabin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana game da Hakkokin Yan-adam a shekarar 1948"

See other formats


Muhimmin Jawabin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana game da 
Hakkokin Yan-adam a shekarar 1948 

Gabatarwa 

Ganin cewa yanci da adalci da zaman lafiya ba za su girku a duniya ba, sai in an amince da 
cewa: dukkan yan-adam suna da mutunci, kuma suna da hakkoki na kowa daidai da na kowa, 
wadanda ba za a iya kwace musu ba, 

Ganin cewa ba abin da ya sa aka aikata abubuwa irin na lokacin jahiliyya wadanda ke tada 
hankalin duniya gaba-daya, ilia rashin sanin hakkokin dan-adam da rena su. Ganin kuma cewa an 
bayyana cewa: muhimmin gurin da yan-adam suka sa gaba shi ne, bayan sun kubuta daga 
tsananin iko da wahala, kowa ya sami damar fadin ra'ayinsa kuma ya sa rai ga abin da zuciyarsa 
ta saka masa, 

Ganin cewa ya kamata a kafa hukumomi wadanda za su kula da kiyayewa da hakkokin yan- 
adam, ta hanyar girka dokoki, domin kada tsananin iko da danniya su yi yawa har su kai mutane 
ga yin kara ko yin tawaye, 

Ganin cewa ya kamata a karfafa aminci tsakanin kasashe, 

Ganin cewa a cikin usular (takardar sharuda) al'ummu, kasashen duniya sun sake nuna 
amincewarsu da muhimman hakkokin yan-adam, da mutuncinsu, da darajar da wadannan halittu 
suke da ita kuma a kan daidai -wa-daida ga namiji da mace, suka kuma dauki alkawalin yin 
kokari domin su kyautata wa yan-adam j in dadin rayuwa a cikin suna kara walawa da yancinsu, 

Ganin cewa kasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta kunsa sun dauki alkawalin cewa: tare da 
hadin gwiwar Majalisar, za su tabbatar da abin da zai sa ko'ina a duniya a kiyaye da dukkan 
muhimman hakkokin yan-adam da dukkan abubuwan da yancinsu ya kunsa, 

Ganin cewa muhimmin abin da zai sa a cika wannan alkawali shi ne, dukkan kasashen duniya su 
zamanto da huska daya za su hangi wadannan hakkokin yan-adam da abubuwan da yancinsu ya 
kunsa, 

Majalisar Dinkin Duniya, a zaman taronta na gaba-daya tafadi cewa: 

Abubuwan da wannan jawabi ya kunsa su zamanto gurin da dukkan al'ummu da kasashen duniya 
suka hadu a kansa kuma suka kokarin cimma, domin kowane mutum da kowane sashen jama'a 
wanda yake da wannan jawabi a ka ko da wane lokaci, ya maida himma ta hanyar tsarin 
makarantu da tarbiyya domin a karfafa kiyayewa da wadannan hakkoki da dukkan abubuwan da 
yancin dan-adam ya kunsa. Bayan haka a yi kokari ta hanyar daukar matakai wadanda za a rika 
ingantawa lokaci zuwa lokaci, kuma wadanda za su shafi kasa daya ko kasashe da yawa domin 
ko'ina a duniya jama'ar kasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta kunsa da ta kasashen da ke 
karkashin mulkin wadansu daga cikinsu ta karbi wannan jawabi, ta kuma yi amfani da shi yadda 
ya kamata. 

Mataki na farko (1) 

Su dai yan-adam, ana haifuwarsu ne duka yantattu, kuma kowannensu na da mutunci da hakkoki 



daidai da na kowa. Suna da hankali da tunani, saboda haka duk abin da za su aikata wa juna, ya 
kamata su yi shi a cikin yan-uwanci. 

Mataki na biyu (2) 

Kowane mutum na da hujjar cin moriyar dukkan abubuwan da yanci ya kunsa da dukkan 
hakkokin da aka bayyana a cikin wannan jawabi ba tare da bambanci ko kadan ba, ko na launin 
fata, ko na zama mace wala namiji, ko na harshe, ko na addini, ko na ra'ayin siyasa, ko kuma 
bambancin ra'ayin da ya shafi kasarsu, ko na zaman jama'a, ko na arziki, ko na haifuwa, ko na 
wani hali daban. 

Bayan haka, ba za a gwada wa mutum wani bambanci ba saboda matsayin kasarsu ko yankinsu a 
fannin siyasa ko na hukunce-hukuncen shari'a ko a huskar kasashen duniya, ko da kuwa kasar 
mai mulkin-kai ce, ko tana karkashin mulkin wata kasa, ko ba ta da cikakken mulkin-kai, ko da 
wani abin da ya rage mata mulki. 

Mataki na uku (3) 

Kowane mutum na da hakkin rayuwa, da zamantowa cikin yanci da samun a kiyaye halittarsa. 

Mataki na hudu (4) 

Ba dan-adam wanda za a sa bauta, kuma doka ta hana bauta da fataucin bayi ta kowane hali. 

Mataki na biyar (5) 

Ba wanda za a yi wa azaba, ko a yi masa hukunci ko horo wanda bai dace da dan-adam ba, ko 
wanda zai kaskanta shi. 

Mataki na shida (6) 

Kowane mutum na da hakkin a ko'ina a san da darajar halittarsa a huskar doka. 

Mataki na bakwai (7) 

Kowa daidai yake da kowa a gaban doka, kuma kowa na da hakkin doka ta yi masa kariya ba 
tare da nuna bambanci ba. Kowane dan-adam kamar kowa, na da hakkin a yi masa kariya game 
da duk wani bambancin da zai saba wa matakan da ke cikin wannan jawabi, da kuma kariya 
game da duk wata manakisa ta sa shi nuna irin wannan bambanci. 

Mataki na takwas (8) 

Kowane mutum, idan ya ga za'a aikata abin da zai hana shi cin moriyar hakkokinsa wadanda 
tsarin mulki ko dokar kasa ta tanada masa, yana da hakkin ya kai kara a gaban hukumar kasarsu 
wadda ke da mukamin yanke hukunci game da irin wannan laifi. 

Mataki na tara (9) 

Ba wanda za'a tsare ko a daure shi, ko kuma a sa shi gudun-hijira ba gaira ba saba. 



Mataki na goma (10) 

Kowane mutum na da hakki a zaman daidai da kowa, na kotu adali kuma mai zaman kansa 
wanda aka kai kararsa a gabansa ya saurari maganar mutumin a cikin adalci kuma a gaban idon 
jama'a, domin kotun nan ne zai kayyade masa hakkokinsa da nauyin da ya rataya a wuyansa, ko 
ya tabbatar da dalilin da ya sa doka ta tuhume shi da laifi kuma za a yi masa hukunci. 

Mataki na goma sha daya (11) 

1 . Duk mutumin da aka tuhuma da aikata wani laifi, zai kasance da matsayin mara-laifi sai 
bayan an yi masa shari'a a gaban idon jama'a wadda ta nuna cewa ya taka doka, ya 
zamanto kuma a lokacin shari'ar an tabbatar masa da kariya wadda za ta kasance 
maceciyarsa. 

2. Ba wanda za a daure saboda ya aikata kuskure ko wani abu wanda dokar kasa ko ta 
kasashen duniya ba ta maida laifi ba a lokacin da ya aikata shi, ko da daga baya ya zama 
babban laifi. Haka kuma, ba za a yi wa mutum hukunci fiye da yadda dokar da ke ci a 
lokacin da ya aikata laifln ta kayyade game da wannan laifi ba, ko da daga baya an sake 
ta. 

Mataki na goma sha biyu (12) 

Ba wanda wani zai shiga sha'aninsa na rayuwa, ko na iyali, ko na mahalli, ko na wasiku ba tare 
da yardarsa ba, ko kuma a ci masa mutunci ko bata masa suna. Kowa na da hakkin doka ta yi 
masa kariya game da irin wadannan abubuwa. 

Mataki na goma sha uku (13) 

1 . Kowane mutum na da hakkin yin kai-da-kawowa cikin yanci, ya ma zauna wurin da yake 
so a cikin wata kasa. 

2. Kowane mutum na da hakkin ya fita daga kowace kasa, har da kasarsu kuma yana da 
hakkin komowa kasarsu. 

Mataki na goma sha luiclu (14) 

1 . Idan azaba ta kai wa mutum karo, yana da hakkin ya tambayi wadansu kasashe gudun- 
hijira kuma ya same shi da matsayin dan gudun-hijiran da doka ta hana a taba. 

2. Mutumin ba zai iya yin amfani da wannan hakki ba idan ana nemansa bayan an tabbata 
ya aikata babban laifi irin wanda doka ta hana ko wanda ya saba wa manufar Majalisar 
Dinkin Duniya da ka'idodinta. 

Mataki na goma sha biyar (15) 

1 . Kowane mutum na da hakkin kasancewa dan wata kasa. 

2. Ba wanda za a tube wa rigarsa ta dan-kasa ba tare da cikakken dalili ba, ko a hana masa 
yin amfani da hakkinsa na sake kasa idan ya ga dama. 



Mataki na goma sha shida (16) 

1 . Idan mace da namiji sun isa aure, suna da hakkin su ami juna su yi iyali, kuma za a yi 
auren ba tare da an rage wa waninsu darajarsa ta dan-adam ba saboda launin fatarsa ko 
don yana dan wata kasa ko kuma don addininsa. Kuma za su kasance da hakkoki na 
namiji daidai da na mace a game da wannan aure, a cikin zaman auren ko a lokacin 
rabuwa idan ta faru. 

2. Ba za a daura auren ba sai kowane daga cikin angwayen ya bada yardarsa cikin yanci. 

3. Shi dai iyali shi ne muhimmin tushen jama'a, saboda haka ya kamata jama'a da hukuma 
su kiyaye shi. 

Mataki na goma sha bakwai (17) 

1 . Kowane mutum, ko shi daya ko a cikin tarayya, yana da hakkin ya mallaki dukiya. 

2. Ba wanda za a kwace wa dukiyarsa ba tare da cikakken dalili ba. 

Mataki na goma sha takwas (18) 

Kowane mutum na da hakkin ya sami yancin yin tunani da na sanin yakamata da na bin addini; 
saboda haka yana da yancin sake addini ko ra'ayin da ya bada gaskiya gare shi, da kuma yancin 
nuna addininsa ko ra'ayinsa, shi daya ko a cikin taro kuma a flli ko a boye ta hanyar koyarwa ko 
yin ibada, ko bauta wa abin da ya bada gaskiya gare shi da yin abubuwan da abin da yake bauta 
wa din ya nuna masa. 

Mataki na goma sha tara (19) 

Kowane dan-adam na da hakkin ya sami yancin kasancewa da ra'ayin kansa da yancin fadar 
ra'ayin nasa; saboda haka yana da hakkin ya sami yancin kauda duk wani tsoro game da 
ra'ayoyinsa, da yancin neman labaru da sababbin ra'ayoyi, ya same su kuma ya baza su duk inda 
yake so ba tare da sanin iyaka ba, kuma ta kowace hanya. 

Mataki na ashirin 20 

1 . Kowane mutum na da hakkin ya sami yancin yin taro da kafa kungiyoyi tare da 
makamantansa muddin dai kungiyoyin na zaman laflya ne. 

2. Ba wanda za a tilasta wa shiga wata kungiya. 
Mataki na ashirin da daya (21) 

1 . Kowane mutum na da hakkin kasancewa a cikin ja-gorancin harkokin jama'a na kasarsu, 
ko shi da kansa ko ta hanyar aika wakilansa wadanda ya zaba cikin yanci. 

2. Kowane mutum na da hakki' a cikin sharadin daidai -wa-daida ya sami halin a daukaka 
shi ya kama ragamar tafiyar da wadansu ayyukan kasarsu na kula da harkokin jama'a. 

3. Yadda al'umma ke so ne mahakunta za su tafiyar da mulkin kasa; za a san bukatar 
al'umma game da mulki ta hanyar gudanar da zabe kan gaskiya lokaci zuwa lokaci, inda 



dukkan yan-kasa a zaman daidai-wa-daida muddin dai suna cikin sharadi, su sami damar 
zartar da zaben kuma cikin an yi jefa kuri'a a asirce ko ta wata hanya mai kama da haka, 
domin a tabbata cewa kowa ya yi zabe cikin yanci. 

Mataki na ashirin da biyu (22) 

Kowane mutum, a matsayinsa na kasancewa daya daga cikin halittun da jama'a ta kunsa, yana da 
hakkin a tabbatar masa da jin dadin rayuwa; ma'anar tabbatar wa dan-adam da jin dadin rayuwa 
shi ne: dangance da tsarin kowace kasa da halin da take da shi, kowane taliki, da kokarin kasarsu 
da taimakon kasashen duniya, ya ci moriyar hakkokinsa na samun biyan bukatunsa game da 
tattalin arziki, da jin dadin jama'a, da al'adu, domin wadannan abubuwa ne ke tabbatar masa da 
mutunci kuma suke daukaka darajar halittarsa cikin walawa. 

Mataki na ashirin da uku (23) 

1 . Kowane mutum na da hakkin ya sami aiki, da yancin ya zabi aikin da yake so dangance 
da kwarewarsa, ya kuma yi aikin kamar kowa a cikin sharadi gwargwado, kuma yana da 
hakkin a kiyaye shi da rashin aiki. 

2. Dukkan yan-adam, ba tare da wani bambanci ba, suna da hakkin su sami kimar albashi 
daya idan aiki daya suke yi. 

3. Duk wanda ke aiki na da hakkin ya sami albashi gwargwadon guminsa, wanda zai biya 
masa bukatunsa na yau da kullum da shi da iyalinsa, kuma irin wadanda suka kamaci 
dan-adam a cikin mutuncinsa. Bayan haka, idan akwai abubuwan da aka tsara don 
kyautata rayuwar jama'a, ya sami yin amfani da su. 

4. Kowane mutum na da hakkin ya kafa kungiyoyin kiyaye sharudan sana'arsa tare da 
makamantansan, ko ya shiga wata kungiya mai irin wannan manufa domin ya tanadi abin 
da zai amfane shi. 

Mataki na ashirin da hudu (24) 

A game da aiki, kowane mutum na da hakkin ya sami hutu don ya shakata da musamman 
kayyadadden wa'adin aiki yadda ba zai raunana masa ba, kuma yana da hakkin ya sami dogon 
hutu lokaci zuwa lokaci wanda a cikinsa zai kasance yana karbar albashinsa. 

Mataki na ashirin da biyar (25) 

1 . Kowane mutum na da hakkin ya sami isasshen halin da zai rayu da shi domin ya kiyaye 
lafiyarsa da shi da iyalinsa, da jin dadin rayuwarsu, ya kuma mallaki halin tabbatar musu 
da abinci da tufafi da mahalli da magani daga likita da sauran abubuwan kyautata rayuwa 
wadanda suke bukata. Har ila yau yana da hakkin a sama masa abin da zai biya wadannan 
bukatu da shi idan ya rasa aikinsa, ko yana rashin lafiya, ko wani musakanci ya same shi, 
ko yana cikin gwaurancin mutuwa, ko tsufa, ko wata ta'adi ko wani hatsari ya raba shi da 
dukiyar da ya tanada yake rayuwa da ita. 

2. Ya kamata a yi wa mata masu ciki da yara kanana tattali da taimako na musamman. 
Kuma dukkan yara ne ya kamata su ci moriyar wannan tattali da taimako, ba wadanda 
aka haifa a cikin aure kadai ba. 



Mataki na ashirin da shida (26) 

1 . Kowane mutum na da hakkin ya sami ilimi. Ya kamata ilimi ya zamanto ba na biya ba a 
kalla a cikin azuzuwan farko, wato tushen ilimi. Tilas ne ga kowa ya yi karatu a cikin 
azuzuwan farko. Ya kamata a baza ilimin husaha da na koyon sana'a a ko'ina. Duk wanda 
kwazonsa ya ba hali ya kamata a ba shi damar zuwa neman ilimin koli ba tare da 
bambanci ba. 

2. Abin nufi ga ilimi shi ne: ya sama wa dan-adam jin dadin rayuwa da karfafa kiyayewa da 
hakkokinsa da muhimman abubuwan da yancinsa ya kunsa. Ya kamata ilimi ya kawo 
fahimtar juna da ragowa da aminci tsakanin kasashe da tsakanin yan-adam, kome launin 
fatarsu da addinin da suke bi, ya kuma karfafa kokarin da Majalisar Dinkin Duniya take 
yi domin a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. 

3. Game da neman ilimi, iyayen ne a gaba wajen hakkin fadin irin tarbiyyar da za a yi wa 
yayansu. 

Mataki na ashirin da bakwai (27) 

1 . Kowane mutum na da hakkin bada gwargwadon gudummuwarsa cikin yanei ga dukkan 
al'amurran al'adu na da'irarsa da ein moriyar abubuwan da ake kagowa don dadada rai, da 
taimakawa ga ci-gaban kimiyya, haka kuma yana da hakkin ya yi amfani da hikimomin 
da da'irarsu ta tanada, da kyakkyawan sakamakon da aka samu daga kimiyya. 

2. Kowa na da hakkin a yi masa kariya ta kowane hali, domin ya sami damar yin fara'a da 
cin amfanin abin da ya kirkiro a fannin kimiyya ko na adabi ko na hikima. 

Mataki na ashirin da takwas (28) 

Kowa na da hakkin ganin an sami kyakkyawan shiri a cikin zaman jama'a da tsakanin kasashen 
duniya domin hakkokin nan da dukkan abubuwan da yanci ya kunsa wadanda aka bayyana a 
cikin wannan jawabi su tabbata sosai. 

Mataki na ashirin da tara (29) 

1 . Dan-adam na da nauyin bauta wa da'irar da yake rayuwa a ciki a wuyansa, domin a nan 
kadai ne yake samun halin karfafa darajarsa ta dan-adam cikin yanci. 

2. Kowa zai yi amfani matuka da hakkokinsa da abubuwan da yancinsa ya kunsa ba tare da 
wata iyaka ba, sai fa wadda doka ta kafa musamman domin a cikin zaman jama'a wadda 
ta san ma'anar dimukiradiyya, kowa ya san kuma ya kiyaye da hakkokin makamantansa 
da abubuwan da yancinsu ya kunsa, kuma domin da'a da kyakkyawan shirin jama'a da jin 
dadin rayuwa ga kowa su tabbata kamar yadda ya kamata. 

3. Ta kowane hali ba za a iya yin amfani da wadannan hakkoki da abubuwan da yanci ya 
kunsa ba a cikin saba wa manufar Majalisar Dinkin Duniya da ka'idodinta. 

Mataki na talatin (30) 

Ba wani mataki a cikin wannan jawabi, wanda wata kasa ko wata kungiya ko wani mutum zai yi 



amfani da shi, ya kwatanta cewa matakin ya ba shi ikon tafiyar da wata hidima, ko aikata wani 
abu da nufin rushe wadannan hakkoki da abubuwan da yanci ya kunsa, wadanda aka bayyana a 
cikin wannan jawabi.